in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bukaci mambobin WTO da su kiyaye ciniki tsakaninsu
2017-12-11 09:49:01 cri

Kasar Sin ta shawarci mambobin hukumar cinikin duniya wato WTO da su kare matsayin gamayyar cinikayya dake tsakaninsu, kana su hada gwiwa wajen gina wani tsari da zai bude kofar bunkasa tattalin arzikin duniya.

Da yake jawabi a lokacin taron musayar ra'ayoyi game da shirin da kasar Sin ta shirya ga kasashe masu karancin ci gaba mai taken "China Program" a lokacin taron koli na WTO a Buenos Aires, ministan kasuwanci na kasar Sin Zhong Shan, ya bayyana cewa, kasarsa za ta kara samar da sabbin tsare tsare da suka shafi bude kofa, domin goyon bayan tsarin gamayyar cinikayya da kuma karfafa gwiwa wajen bude kofa don gina tattalin arzikin duniya.

Ya kara da cewa, kawar da talauci batu ne da ya shafi yin hadin gwiwa kansa don gina al'umma, kana mambobin WTO suna da rawar da za su taka wajen hada karfi da karfe don cimma nasarar ajandar dawwamamman ci gaba nan da shekarar 2030. Ya ce, wannan ya nuna a fili cewa, akwai bukatar a ba da fiffiko ga kasashen duniya masu karancin ci gaba da kuma taimakawa mutanen dake rayuwa cikin matsanancin talauci domin inganta rayuwar bil adama baki daya.

Da yake jawabi game da shirin na kasar Sin, Zhong ya nanata cewa, kasar Sin tana zaburar da kasashen dake da koma bayan ci gaba da su shiga gamayyar hukumar ciniki ta WTO, kuma su nemi taimako daga dukkan bangarorin da abin ya shafa.

Darakta janar na WTO Roberto Azevedo, ya bayyana wannan dandali da kasar Sin ta samar wanda ya ba da damar shiga tattaunawa don yin musayar kwarewa da gabatar da wasu tsare tsare don taimakawa kasashen matalauta su ci gajiyar gamayyar ta WTO.

Ya kara da cewa, kasashen masu karancin ci gaba 6 ne suka shiga hadakar ta WTO a cikin shekaru 5 da suka gabata, hakan ya nuna muhimmancin gudumowar da kasar Sin ke baiwa gamayyar kasuwancin kasa da kasa.

Kasar Sin da WTO, sun kulla yarjejeniyar kafa shirin "China Program" ne a watan Yulin shekarar 2011.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China