in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar 'yan kasuwar Sin ta isa Habasha
2017-06-20 10:23:50 cri

Tawagar wakilan kamfanoni 70 daga birnin Shenzhen, cibiyar kasuwanci ta kasar Sin, ta isa Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha domin halartar taron baje kolin kayayyaki da kulla dangantakar kasuwanci.

Wakilan sun halarci kasar ta gabashin Afrika ne, don halartar taron zuba jari na yan kasuwar birnin (Shenzhen), da kuma baje kolin kayayyaki tsakanin ranar Litinin zuwa Talata.

Lu Pengqi, mataimakin shugaban kwamitin raya kasuwanci ta kasa da kasa na kasar Sin (CCPTI), ya ce, akwai dalili mai kyau game da ziyarar tawagar 'yan kasuwa na Shenzhen.

Lu ya ce, birnin Shenzhen yana da karfin tattalin arziki na GDP da ya kai dala biliyan 283 a shekarar 2016, birnin ya kasance daya daga cikin yankin mafi arziki na kasar Sin.

Shenzhen yana da yawan al'umma miliyan 12, kuma akwai masana'antun Sinawa da yawansu ya zarta 5,300, ciki har da manyan kamfanonin nan na kimiyya da suka hada da Huawei, ZTE, da Tencent, baki daya sun zuba hannun jari a kasashen ketare da ya kai dala biliyan 80.

Kasar Habasha ta baiwa Shenzhen babbar damar gudanar da kasuwanci a nahiyar Afrika a nan gaba, saboda irin sha'awar da kasar ta nuna ta bunkasuwar masana'antu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China