in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yankin masana'antu da Sin ta gina a Habasha na gab da fara aiki
2017-12-07 09:52:01 cri

Hukumomi a Habasha sun ce, yankin masana'antu na Kombolcha (KIP) dake jihar Amhara na arewacin kasar, zai fara aiki cikin watan Fabrerun shekarar 2018.

An kaddamar da yankin da kamfanin gine-gine na kasar Sin ya gina a watan Yulin da ya gabata, inda aikin ginin ya lakume dala miliyan 90 tare da mamaye kadada 75 na fili.

Daraktan kula da aikin KIP Azmeraw Dejene, ya shaidawa manema labarai cewa, da zarar ya fara aiki, ana sa ran zai dauki mutane 20,000 aiki tare da jan hankalin kamfanonin sarrafa tufafi daga kasashe kamar su Sin da Amurka da Koriya ta kudu.

KIP dake da nisan kilomita 376 daga arewancin Addis Ababa, babban birnin Habasha, wani bangare ne na kokarin kasar na raya hanyar masana'antu dake kan layin dogon da ya hada kasar da tashar ruwan Djibouti.

Da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ministan sufurin Habasha Ahmed Shide, ya ce yankin masana'antun dake kan layin dogon da ya hada Habasha da Djibouti, zai taka muhimmiyar rawa wajen sauya tsarin tattalin arziki ta hanyar taimakawa wajen saukaka sufurin kayayyaki. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China