in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude bikin baje kolin fina-finan Sin a Habasha
2017-09-26 10:01:02 cri

An bude bikin baje kolin fina-finan kasar Sin jiya Litinin a birnin Addis Ababa na Habasha, a wani bangare na bikin makon al'adu na kasar Sin.

Da yake ganawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, jami'in kula da harkokin al'adu a ofishin jakadancin kasar Sin dake Habasha Yan Xiangdong, ya ce baje kolin fina-finan wanda ba a taba shirya irinsa ba a Habasha, zai nuna daddaden tarihin wayewar kan kasar Sin ga al'ummar Habasha wadanda su ma ke tunkaho da makamancin tarihin.

Yan Xiangdong ya ce, fina-finan 6 da za a nuna a wannan makon, na da nufin kawar da tunanin galibin al'ummar Habasha da suka dauka fina-finan Sinawa fina-finai ne na fada daga Hong Kong.

A nasa bangaren, fitaccen 'dan wasan fim na kasar Habasha kuma mataimakin shugaban kungiyar masu shirya fina-finai ta kasar Desalegn Hailu, ya amince cewa, nuna fina-finai da 'yan wasan Sinawa, ita ce hanya mafi dacewa ta bayyana al'adu daban-daban na kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China