Gwamnan jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya Kashim Shettima, ya yi kira ga Sinawa su kara zuba jari a yankin.
Kashim Shettima ya shaidawa jakadan kasar Sin a Nijeriya Zhou Pingjian cewa, yankin da tattalin arzikinsa ba shi da karfi kamar da, zai iya farfadowa nan ba da dadewa ba, da taimakon masu zuba jari na kasar Sin.
Yankin na arewa maso gabashin Nijeriya ya shafe shekaru 7 yana fama da ayyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram.
Gwamnan wanda ya kawo ziyara kasar Sin sau da dama, ya ce kasar na taka rawar gani wajen samar wa nahiyar Afrika kyakkyawar makoma.
A nasa bangaren, jakada Zhou Pingjian, ya ce kasar Sin za ta ci gaba da tabbatar da cewa, ita aminiya ce ta Nijeriya cikin ko wane hali da ta samu kanta.
Ya ce, Sin da Nijeriya za su ci gaba da da hada hannu a bangarori da dama, inda ya ce, kamfanonin kasarsa da dama sun nuna sha'awar taimakawa yankin na arewa maso gabashin Nijeriya.
Kafin ziyarar ta sa da gwamnan jihar Borno, jakadan ya halarci bikin samar da dala miliyan 5 ga ayyukan jin kai a yankin na arewa maso gabas, a wani bangare na tallafin kasar Sin ga shirin samar da abinci na MDD a yankin. (Fa'iza Mustapha)