in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: An kaddamar da aikin sashi na 2 na layin dogo tsakanin Lagos zuwa Ibadan
2017-03-08 10:17:03 cri

Mukaddashin shugaban kasar Najeriya Yemi Osinbajo, ya kaddamar da aikin bangare na 2, na ginin layin dogo da zai hada birnin Ikon jihar Legas da birnin Ibadan na jihar Oyo a kudu maso yammacin kasar.

Da yake jawabi yayin bikin kaddamar da aikin a jiya Talata, Mr. Osinbajo ya ce, aikin zai kammala ne cikin shekarar 2018, zai kuma taimaka matuka wajen fadada sassan tattalin arzikin Najeriya.

Mukaddashin shugaban kasar ya kara da cewa, wannan aiki na cikin alkawuran da gwamnati mai ci ta yiwa al'ummar kasar, yayin yakin neman zaben ta. Bugu da kari an sanya aikin gyaran layin dogon da ya hada jihar Legas da jihar Kano dake arewacin kasar cikin kasafin kufin shekarar nan ta 2017.


1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China