in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bikin Kung Fu na Sin ya ja hankalin mutane a Lagos na Nijeriya
2018-05-07 10:02:34 cri

Mamamkon ruwan sama, bai zama tarnaki ba, ga dandazon mutanen da suka taru a Lagos, cibiyar hada-hadar kasuwanci ta Nijeriya, domin kallon bikin Kung Fu na kasar Sin a ranar Asabar da ta gabata.

Kamfanin StarTimes na kasar Sin mai samar da Fina-finan talabijin a nahiyar Afrika da hadin gwiwar bankin UBA ne suka shirya bikin, irinsa na farko, wanda ya gudana daga ranar 14 ga watan Afrilu, zuwa 5 ga watan nan na Mayu.

Duk da ruwan sama mai karfi da ya sauka a birnin, masoya Kung Fu sun nishadantu. Ranar karshe ta bikin da ya shafe makonni 3, ta kayatar sosai, inda dubban jama'ar birnin suka yi wa filin wasanni dake yankin Surulere na jihar tsinke, don ganin wanda zai zamo zakara.

Bikin na Kung Fu shiri ne da aka yi kai tsaye, wanda ke da nufin zurfafa musayar al'adu tsakanin Nijeriya da kasar Sin.

Akalla masu wasannin Kung Fu 14 'yan Nijeriya ne suka nuna bajintarsu a gaban manyan 'yan wasan na kasar Sin da Nijeriya, inda aka zabi mutane 3 da suka yi nasara.

Kamfanin StarTimes ya ce, wadanda suka yi nasarar za su samu damar fitowa a fim din Kung Fu da zai dauka a Nijeriya nan gaba a bana.

Haka zalika, za su samu damar zama taurarin fim a wani jerin fina-finan Kung Fu da za a dauka a kasar Sin, wanda bankin UBA zai dauki nauyi.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China