in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ni dan nahiyar Afirka ne, ina koyar da harshen Sinanci a Afirka
2018-08-28 18:06:09 cri

 

Assalamu alaikum, sunana Nama Didier Dieudonne, ina daga cikin daliban kasar Kamaru na farko da suka kammala karatun koyon harshen Sinanci, kana daya daga cikin malamai na farko da aka tura mu makarantar midil domin koyar da Sinanci. Ni ne kuma dan Afirka na farko da kwalejin Confucius ya dauka a matsayin mai aikin sa kai na koyar da Sinanci a ketare. Hoton dake nuna yadda nake koyar da darasin Sinanci.

Daga shekarar 2011 zuwa 2015, na yi karatun digiri na biyu kan aikin koyar da harshen Sinanci a jami'ar horar da malamai ta lardin Zhejiang, har ma an zabe ni a matsayin fitaccen dalibin jami'ar. Ni ne na biyu daga dama.

Daga shekarar 2013 zuwa 2017, bisa jagorancin Xu Lihua, darektar ofishin kula da aikin koyar da Sinanci da ke jami'ar horar da malamai ta lardin Zhejiang, na hada kan wasu malamai Sinawa muka tsara jerin littattafan koyar da Sinanci mai taken "Kamaru, Assalamu alaikum!", wadanda suka taimaka a fannin koyar da Sinanci a makarantun midil na kasar ta Kamaru.

Ni da wasu malamai da dalibai da suka sayi littattafan koyar da Sinanci.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China