in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta sake nanata kudurinta na shiga shawarar ziri daya da hanya daya
2017-10-26 10:23:23 cri

Kasar Sudan ta sake nanata kudurinta na shiga a dama da ita a shawarar nan ta "Ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta gabatar, ta yadda za ta cimma nasarar manufofin kafa ta.

Mai taimakwa shugaban Sudan kan hadin gwiwar kasashen biyu Awad Ahmed al-Jaz shi ne ya sanar da hakan yayin da yake jawabi a wani taron karawa juna sani mai taken "hadin gwiwar Sin da kasashen Larabawa da shirin hanyar siliki". Ya ce, sassan biyu suna da niyar fadada alakar dake tsakaninsu ta yadda za su ci gajiyar wannan alaka ba tare da tsoma baki a harkokin juna ba.

A jawabinsa jakadan Sin dake Sudan Li Lianhe, ya nanata muhimmancin shawarar ta "Ziri daya da hanya daya" wajen karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen dake yankin, da samar da damammakin shiga a dama da su a shawarar da sauransu.

Shi ma babban darektan gamayyar kungiyoyin abokantaka tsakanin Sin da kasashen Larabawa Ali Yousif Ahmed ya ce, kasashen Larabawa za su ci gajiyar shawarar "Ziri daya da hanya daya", a fannonin ciniyayya, ci gaba mai dorewa, da samar da muhimman kayayyakin more rayuwa.

Manufar shawarar wadda shugaba Xi Jinping ya gabatar a shekarar 2013, ita ce, hade yankunan Asiya da Turai da Afirka dake kan tsohuwar hanyar siliki har ma fiye da haka, ta hanyoyin cinikayya da kayayyakin more rayuwar jama'a.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China