in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci kasashen Afrika su ci gajiyar damarmakin dake tattare da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" ta kasar Sin
2018-05-11 09:38:44 cri
Wani masanin harkokin kasuwanci na kasa da kasa, ya bukaci kasashen Afrika sun ci gajiyar damarmakin dake tattare da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" ta kasar Sin, domin ciyar da kansu gaba.

Da yake ganawa da Xinhua, yayin wani taron yini guda kan zuba jari tsakanin kasashen Ghana da Nijeriya, David Ofosu-Darte, ya bukaci nahiyar ta yi amfani da kudaden da kasar Sin za ta bada karkashin shawarar, ta yadda za ta samar da nata ababen more rayuwa domin inganta cinikayya tsakanin kasashenta.

Shawarar da kasar Sin ta gabatar a shekarar 2013, na nufin yankin kasuwancin da hanyar siliki ta ratsa da hanyar siliki ta cikin ruwa ta karni na 21. Sannan ta na da nufin hada kasashen ta fannonin manufofi da kayakin more rayuwa da cinikayya da hada-hadar kudi da al'ummu daban-daban, don samar da sabon dandalin hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya da samar da hanyoyin samun ci gaba tare, ta yadda karin kasashe da jama'a za su more.

A cewar Ofosu-Dorte, shawarar na da tasiri kan Afrika saboda a yanzu, cinikayya tsakanin kasar Sin da nahiyar Afrika, ta karu daga dala biliyan 10 a shekarar 2000, zuwa dala biliyan 239 a yanzu, a don haka, kasar Sin ta zama babbar abokiyar cinikayyar Afrika.

Har ila yau, ya ce akwai damarmaki da Afrika za ta iya samu, ta hanyar samun kudaden jari daga kasar Sin, domin samar da kayakin more rayuwa da inganta cinikayya tsakanin kasashen nahiyar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China