in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Buhari ya mika sakon ta'aziyar rasuwar Kofi Annan
2018-08-19 16:10:45 cri

A safiyar jiya ne aka bayar da rahoton rasuwar tsohon babban sakataren MDD Kofi Annan a wani asibitin Switzerland, ya rasu yana da shekaru 80 a duniya. Shugaban tarayyar Najeriya Buhari ya aikawa shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo sakon ta'aziya, inda ya isar da alhini da ta'aziya ga gwamnatin kasar da al'ummar kasar bisa rasuwar Kofi Annan. Shugaba Buhari ya bayyana Kofi Annan a matsayin dattijo mai hali na gari, wanda ya ba da babbar gudumowa wajen shimfida zaman lafiya da samun ci gaba a fadin duniya.

Kofi Annan ya kasance babban sakataren MDD tsakanin shekarar 1997 zuwa 2006, ya taba lashen lambar yabon zaman lafiya ta Nobel a shekarar 2001, haka kuma kokarin da ya yi wajen yaki da talauci da kyautata aikin ba da ilmi da kawar da cutar kanjamau da daga matsayin mata da ingiza kwaskwarima a MDD da tabbatar da zaman lafiyar duniya ya samu yabo matuka daga wajen al'ummun kasashen duniya baki daya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China