in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Najeriya sun mika yara 23 da aka ceto ga UNICEF
2018-08-19 16:29:18 cri

A jiya Asabar rundunar sojojin Najeriya ta sanar da cewa, ta mika yara kimanin 23 wadanda ta yi nasarar ceto su daga hannun mayakan Boko Haram a jihar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriyar ga hukumar tallafawa ilmin yara ta MDD wato UNICEF.

Wannan tsari ya yi daidai da tsarin da ake gudanarwa a kasa da kasa, in ji Abbah Dikko, kwamandan rundunar sojoji masu wanzar da zaman lafiya ta Lafiya Dole, inda ya bayyana hakan a yayin wani kwarya-kwaryar biki da aka shirya a birnin Maiduguri.

Ya kara da cewa, manufar wannan shirin ita ce domin kyautata alakar dake tsakanin dakarun sojojin da fararen hula a yunkurin samar da dawwamamman zaman lafiya a shiyyar arewa maso gabashin kasar.

A nasa tsokacin, Geoffrey Ijumba, jami'in hukumar UNICEF dake wakilci a jihar Borno, wanda ya karbi yaran, ya yi maraba da sakin yara 23 maza da mata wadanda shekarunsu suka kama daga 12 zuwa 17 dake karkashin kulawar jami'an sojojin.

Pernille Ironside, mai rikon mukamin wakilin UNICEF a Najeriya, ya jaddada cewa, MDD za ta ci gaba da yin aiki tare da sojojin da sauran hukumomin da abin ya shafa wajen tallafawa dukkan yaran da dakarun sojojin suka mika domin maido da su cikin hayyacinsu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China