Shugaban Amurka Donald Trump, ya bukaci sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo, ya soke tafiyar da ya yi niyyar yi zuwa Koriya ta Arewa wato DPRK, yana mai dogaro da rashin samun ci gaba game da batun kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya.
Donald Trump ya wallafa a shafinsa na Tweeter a jiya cewa, ya bukaci Mike Pompeo ya soke ziyararsa zuwa Koriya ta Arewa a wannan lokaci ne saboda yana ganin ba su samu gamsasshiyar ci gaba game da batun kawar da makaman nukiliya ba.
Ya kara da cewa, sakatare Pompeo na sa ran zuwa Koriya ta Arewa a nan gaba.
Har ila yau, ya ce ya na mika sakon gaisuwa da ban girma ga shugaba Kim. Kuma yana sa ran ganinsa nan ba da dadewa ba. (Fa'iza Mustapha)