in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da taro kan ci gaban kafafen sadarwa na zamani a Nijeriya
2018-08-14 10:23:45 cri

An kaddamar da taro na farko kan ci gaban kafafen sadarwa na zamani jiya Litinin a Abuja, fadar mulkin Nijeriya, inda ya samu mahalarta da suka hada da kwararru kan kafafen sadarwa na zamani daga ciki da wajen kasar da kuma 'yan kasuwa.

An shirya taron na yini 3 ne domin magance matsalolin da suka shafi kafafen sadarwa na zamani, da suka hada da yada labaran bogi da kuma yadda za a yi amfani da intanet ta hanyoyin da suka dace.

Mashirya taron sun shaidawa Xinhua cewa, wasu daga cikin makasudin shirya taron sun hada da hada jama'a da kuma yin muhawara kan abubuwan dake bullowa ta kafofin, da ma wayar salula.

Daya daga cikin masu jawabi a wajen taron, Shahud Hameed Dawood dan kasar Malaysia, ya ce kafafen sadarwa na zamani na samun ci gaba sosai, ta yadda babu wanda ba ya amfani da su. Yana mai cewa, idan kana son kauracewa kafafen, to ba za ka san abubuwan dake faruwa a duniya ba.

Ya kara da cewa, aikinsu shi ne, ilimantar da al'ummar Nijeriya game da amfani da shirye-shiryen kafafen sadarwa na zamani da kuma koya musu yadda za su yi amfani da su yadda ya kamata, har ma da yadda za su yi amfani da su wajen samun kudi.

Mahalarta taron da galibinsu matasa ne 'yan kasa da shekaru 40, sun lalubo hanyoyin samun ci gaba a kafafen, ba kadai ta fuskar nishadi ba, har da samu ilimi da damarmakin samun kudi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China