in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata Amurka ta rika hulda da masu zuba jari na Sin bisa adalci da gaskiya
2018-08-14 13:50:32 cri

Ma'aikatar kula da harkokin cinikayya ta kasar Sin na fatan Amurka za ta rika hulda da Sinawa masu zuba jari bisa gaskiya da adalci, a yayin da za ta rika bibiyar tasirin dokar zuba jari ta kasashen waje ta Amurka a kan kamfanonin kasarta.

Kakakin ma'aikatar ne ya bayyana haka, lokacin da yake tsokaci bayan shugaban Amurka Donald Trump, ya sanya hannu kan kasafin kudin kasar na shekarar 2019, wanda ya kunshi dokar nazarin hadarin jarin kasashen waje da aka yi wa gyaran fuska.

Ya ce, kasar Sin za ta yi cikakken nazari kan dokar tare da bibiyar tasirinsa kan kamfanoninta.

Yayin da dunkulewar tattalin arzikin duniya ke dada fadada, zuba jari tsakanin kasa da kasa na kara habaka. Zuba jari tsakanin kasashen biyu na tattare da dimbin damarmaki, la'akari da kudurin kamfanonin kasashen biyu na kara inganta hadin gwiwa.

Jami'in ya ce, ya kamata gwamnatocin biyu sun rika girmama muradun juna tare da samar da kyakkyawan yanayin mai karfi. (Fa'iza Mustpaha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China