in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi: Lawrence Kudlow ya ba da ra'ayi ba tare da tushe ba
2018-08-04 21:11:41 cri

A sakamakon tsananta rikicin ciniki daga bangare guda da Amurka ta yi, hukumar kula da harkar sanya haraji ta majalisar gudanarwar kasar Sin ta tsai da kuduri a jiya cewa, za ta kara sanya harajin kaso 25 bisa dari ko kaso 20 bisa dari ko kaso 10 bisa dari ko kuma kaso 5 bisa dari, kan kayayyakin Amurka wadanda darajarsu ta kai dalar Amurka kusan biliyan 60. Direktan kwamitin tattalin arziki na fadar shugaban kasar Amurka Lawrence Kudlow ya bayyanawa kafofin watsa labaru cewa, ya yi wa kasar Sin kashedin cewa, gwamnatin Trump ta na da karfin cika alkawarin ciniki, kana ya ce, Amurka za ta kafa wani kawance cikin sauri don tinkarar matakan da kasar Sin ta dauka kan wannan batu.

Ma'anar Kudlow ita ce yin kashedi ga kasar Sin cewa shugaba Trump zai kara gabatar da matakai masu karfi. A wannan mako, Amurka ta tsai da kudurin kara harajin kaso 25 bisa dari, kan kayayyakin dake shiga kasar daga kasar Sin, wadanda darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 200, don haka kasar Sin ta dauki matakai don mayar da martani. Wannan ya shaida cewa, kashedin da Amurka ta yiwa kasar Sin ba shi da amfani. Amurka ta fi son yin amfani da karfinta na mallakar kasuwa mafi girma a duniya don warware matsaloli. Amma a shekarar 2018, kasar Sin za ta kasance kasar da ta mallaki kasuwa kamar Amurka, watakila ma ta zarce Amurkar, hanyar da kasar Amurka ta kan bi, ba ta da amfani ba ga kasar Sin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China