in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na sa ran ciyar da huldar abokantaka da Afirka ta kudu
2018-05-30 19:09:55 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, bana ake cika shekaru 20, da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Afirka ta kudu, a don haka kasar Sin ke sa ran za a ciyar da huldar abokantaka tsakanin sassan biyu gaba daga dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare.

Hua Chunying ta bayyana hakan ne a yau Laraba, yayin taron manema labaran da aka saba gudanarwa. Ta ce mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi zai ziyarci Afirka ta kudu a farkon watan Yunin dake tafe, kuma zai halarci taron ministocin harkokin wajen kasashen mambobin kungiyar BRICS da za a shirya a kasar. Hua ta kara da cewa, yayin ziyarar da zai gudanar, Wang Yi zai yi musanyar ra'ayoyi kan manyan batutuwa da hukumomin kasar Afirka ta kudu, misali ganawar da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai yi da sauran shugabannin kasashen BRICS a Johannesburg, da hahaltar shugaban kasar Afirka ta kudu Matamela Cyril Ramaphosa, taron kolin birnin Beijing na dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, da dai sauransu. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China