in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabar UNICEF ta kadu da hari ta sama da ya aukawa motar dalibai a arewacin Yemen
2018-08-10 10:15:44 cri

Shugabar asusun kula da kananan yara na MDD wato UNICEF, ta yi tir da hari ta sama da ya samu motar dalibai a arewacin Yemen a jiya Alhamis, al'amarin da ya yi sanadin mutuwar yara sama da 20.

Daraktar zartarwa ta UNICEF Henrietta Fore, ta ce hari kan yara abu ne da ba za a taba amincewa da shi ba. Ta ce, ta kadu da rahoton harin da aka kaiwa yaran da ba su ji ba, ba su gani ba, tana mai cewa, abun ya isa haka nan.

Harin ya samu motar daliban ne a wata kasuwa dake Dahyan na lardin Saada dake arewacin kasar. Yayin da har yanzu ba a tabbatar da adadin wadanda suka mutu ba, rahotannin farko na nuni da cewa, adadin na iya zarta 60, inda kuma wasu da dama suka jikkata. Rahotanni na cewa, galibin yaran 'yan kasa da shekaru 10 ne.

Henrietta Fore, ta yi kira ga bangarori masu rikici da juna, su mutunta dokokin kasa da kasa, su kuma kyale yara da fararen hula da kadarorinsu domin kare kasar daga kara fadawa cikin mawuyacin hali da matsalolin jin kai da take fuskanta cikin sama da shekaru 3 da suka gabata. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China