in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi tir da kwantan baunar da ake ci gaba da yi wa jerin gwanon motocin ba da agajin jin kai a Nijeriya
2017-12-19 10:29:17 cri

Ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD, ya yi tir da kwantan baunar da ake ci gaba da yi wa jerin gwanon motocin dake dauke da kayakin abincin mutanen da rikici ya rutsa da su a yankin arewa maso gabashin Nijeriya.

Wata sanarwa da shugabn ofishin a Nijeriya Edward kallon ya fitar, ta ce harin da aka kai wa motocin agajin jin kai a ranar 16 ga watan Disamba da wadanda aka kai a baya, na barazana ga isar kayayyakin ceton rai ga al'ummar dake cikin bukata a yankin na Nijeriya.

Sanarwar ta ce, kwantan baunar ta baya-bayan nan da kungiyar 'yan ta'adda ta yi a titin dake tsakanin Dikwa da Gamboru a yankin arewa maso gabashin jihar Borno, ya janyo asarar rayukan fararen hula a kalla 4.

A cewar Edward Kallon, harin ya kuma lalata kayayyakin bukata dake da nufin rage radadin dubban mata da maza da kuma yara.

Ya ce, dole ne a tabbatar da kare rayuka da lafiyar jami'an ba da agaji da motocinsu a fadin yankin arewa maso gabashin Nijeriya, ta yadda mutanen dake bukatar taimako za su samu isassun kayayyakin agaji a kan lokaci, yana mai cewa, rayuka da dama ne ke cikin hatsar

MDD da abokan huldarta na aiki ne a yankin arewa maso gabashin Nijeriya domin samar da agajin jin kai ga mutane miliyan 6.9 da rikici ya rutsa da su. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China