in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD na kara kaimi wajen kai agajin jin kai Nijeriya
2017-10-20 09:36:43 cri

Ofishin MDD mai kula da agajin jin kai, ya ce ayarin jami'ansa na kara kaimi wajen kai agajin da ya kunshi abinci da sinadaran gina jiki a yankin arewa maso gabashin Nijeriya dake fama da rikici.

Ofishin ya ce, ana gudanar da aikin ne bisa ingantuwar kayayyakin aiki da hadin gwiwa tsakanin fararen hula da sojoji.

Wata sanarwa da ofishin ya fitar, ta ce a yanzu, jami'an na iya kaiwa wasu yankuna da a baya ba sa iya shiga.

A cewar hukumar, a ko wane wata, mutane miliyan biyu ne ke samun tallafin abinci ko kuma kudin abinci a yankin.

Ta ce, a bana, abokan huldar hukumar sun samu kai wa ga yara 500,000 da mata masu juna biyu da masu shayarwa ta hanyar shirye-shiryen ciyarwa.

Da farko, hukumar ta bayyana damuwa kan yadda yanayin jin kai a yankin ya fi na ko ina a duniya kamari.

Matsalar da rikicin Boko Haram ya haifar, musammam a yankin arewa maso gabashin kasar, ya jefa mutane miliyan 8.5 cikin matsananciyar bukatar agaji a jihohin Borno da Adamawa da kuma Yobe. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China