in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala taron dandalin matasan Sin da Afrika a Shenzhen
2018-05-27 20:46:24 cri

A yau Lahadi aka kammala taron dandalin matasan Sin da Afrika a birnin Shenzhen dake kudancin kasar Sin, inda aka tabo muhimmancin rawar da shugabannin matasa za su taka wajen ci gaban al'umma.

Taron dandalin matasan na Afrika da Sin karo na 4, an gudanar da shi ne a birnin Shenzhen na lardin Guangdong. Sama da shugabannin matasa 70 daga kasashen Afrika kimanin 40 ne suka halarci taron na wuni biyu.

Song Tao, shugaban sashen hulda da kasashen duniya na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin CPC, ya bukaci matasan na kasashen Sin da Afrika da su sadaukar da kansu domin ci gaban kasashensu, kuma su ba da gudunmowa wajen kyautata hadin kan kasashen Sin da Afrika.

Mahalarta taron sun ba da shawarwari a wasu bangarori da suka hada da karfafa musayar bayanai da hadin gwiwa tsakanin kungiyoyin matasan, ta yadda za'a samu karfafuwar dangantaka tsakanin Sin da kasashen Afrika.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China