in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana ta nemi sulhu da hukumar FIFA
2018-08-16 10:06:43 cri

Gwamnatin kasar Ghana ta maida martani ga kurarin da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta yi, cewa za ta dakatar da kasar daga duk wata harka da ta shafi tamaula, inda Ghanan ta ce, ta dauki matakin rushe hukumar kwallon kafar kasar ne, domin kare doka, da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Cikin wata wasika da ministan matasa da wasanni na kasar Ghana Isaac Kwame Asiamah ya sanyawa hannu, gwamnatin kasar ta ce, tana fatan warware sabanin ta da hukumar ta FIFA ta hanyar shawarwari.

Mahukuntan Ghana, sun ce ba su da wani buri na tsoma baki cikin harkokin wasannin kasar, amma kuma rushe hukumar wasan kwallon kafar kasar na da nasaba da kare dokokin cikin gida, tare da tabbatar dakile yaduwar cin hanci da rashawa, da sauran dabi'u na karya doka a cikin kasar.

Wasikar ta kara da cewa, ko shakka babu gwamnatin Ghana ta fahimci kudurin hukumar FIFA, game da bunkasa harkokin gudanarwar kwallon kafa a kasar, da dakile karya dokokin ta hanyar almundahana, da cin hanci ka karbar na goro, wanda hakan ya yi daidai da manufofin gwamnatin kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China