in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban CAF na goyon bayan Morocco wajen neman karbar bakuncin gasar wasan kwallon kafa na kofin duniya na shekarar 2026
2018-01-13 13:55:34 cri
Shugaban kungiyar wasan kwallon kafa ta kasashen Afirka CAF Ahmed Ahmed ya ce, zai nuna cikakken goyon baya ga kasar Morocco wajen neman karbar bakuncin gasar wasan kwallon kafa na cin kofin duniya na shekarar 2026.

Ahmed ya bayyana haka ne a yayin taron manema labaru da aka shirya a jiya Juma'a a Casablanca, inda ya ce, a matsayinsa na shugaban kungiyar CAF, yana da nauyin goyon bayan Morocco bayan da ta tsaida kudurin neman karbar bakuncin gasar wasan kwallon kafa na cin kofin duniya. Ya kuma kara da cewa, kamar yadda kowa ya sani ne, nahiyar Afirka ta samu nasarar a zo a gani a fannin wasan kwallon kafa, amma nahiyar ta karbi bakuncin gasar wasan kwallon kafa na duniya karo guda ne kawai, idan kasar Morocco ta samu damar karbar bakuncin gasar, to za a sake kawo gasar a Afirka.

A watan Agustan bara, kungiyar kwallon kafa ta kasar Morocco ta mika bukatar a hukumance ga kungiyar FIFA na neman karbar bakuncin gasar wasan kwallon kafa na cin kofin duniya na shekarar 2026. Kasar ta taba neman wannan damar har sau hudu a shekarun 1994, da 1998, 2006 da kuma 2010, amma ba ta samu nasara ba. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China