in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan takarar neman shugabancin FIFA na neman kari'un shugabannin shiyyoyi
2016-01-14 10:18:15 cri

Yan takara biyu dake neman shugabancin kungiyar kwallon kafa ta duniya (FIFA) sun mai da hankali zuwa kasar Ghana a ranar Laraba domin zawarcin kuri'un yammacin Afrika a yayin zaben da zai gudana a wata mai zuwa. Yariman kasar Jordaniya Ali Al Hussein da shugaban kwallon kafar Asiya (AFC), Salman Bin Brahim Al Khalifa sun bayyana a gaban wakilai na kungiyar kwallon kafar wannan shiyya a cibiyar kungiyar kwallon kafa ta yammacin Afrika (UFAO Zone B) dake birnin Accra.

Masu takarar biyu sun yi jawabi ga wakilan wannan kungiya, da zummar janyo hankalin wadannan jami'ai da su kada musu kuri'a a lokacin zaben da zai gudana a ranar 26 ga watan Febrairu a birnin Zurich na Suisse.

Dan kasar Italiya Gianni Infantino, da kuma wakalan Jerome Champagne da kuma 'dan kasar Afrika ta Kudu Tokyo Sexwale, da ya kamata su yi jawabi a gaban wakilan UFAO, ba su je ba. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China