in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi maraba da sake bude mashigin zirin Gaza
2018-08-16 09:55:25 cri

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi maraba da matakin kasar Isra'ila na sake bude mashigin zirin Gaza, tare da fadada yankunan kamun kifi dake gabar kogin dake tsakanin kasar da yankunan Falasdinawa.

Da yake bayyana hakan ta bakin kakakin sa Stephane Dujarric, Mr. Guterres ya ce, yana murnar ganin cewa, masu ruwa da tsaki a matakan warware takaddama tsakanin Isra'ila da al'ummar Falasdinawa sun karbi shawarar kaucewa jefa karin fararen hula mazauna zirin Gaza cikin mummunan yanayi.

Daga nan sai ya sake jaddada kira ga dukkanin sassa, da su mara baya ga aniyar shugaban ayyukan tsare tsare na MDD Nickolay Mladenov, da kasar Masar, wadanda ke kokarin ganin an dakile sake tabarbarewar yanaki a zirin Gaza.

A ranar Laraba ne dai Isra'ila ta sake bude mashigin Kerem Shalom wanda shi ne kadai mashigi da ke iya ba da damar shigar da kayayyakin da doka ta amincewa zuwa Gaza.

Tsakanin ranar 9 ga watan Yuli zuwa 14 ga watan Agusta, Isra'ila ta amince a shigar da kayayyakin abinci, da magunguna, da wani adadi na makamashi zuwa yankin da ta killace, ko da yake ta hana fitar da duk wani nau'in kayayyaki ta mashigin.

Albarkacin wannan dama, ofishin MDD mai lura da ayyukan jin kai ko OCHA a takaice, ya aike da motoci sama da 400 dauke da nau'o'in kayayyaki zuwa zirin na Gaza.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China