in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kashedi game da yiwuwar fuskantar matsanancin yanayin jin kai a Gaza
2018-02-07 13:15:20 cri

MDD ta bayyana damuwa game da matsalar da za a iya fuskanta a yankin zirin Gaza, muddin makamashin da ake amfani da shi a yankin ya kare.

Da yake jawabi game da hakan yayin taron manema labarai na rana rana da ake shiryawa, kakakin MDD Farhan Haq ya rawaito mukaddashin jagoran tsare tsare na MDD game da ayyukan jin kai a yankunan da falasdinawa ke zaune Roberto Valent na cewa, akwai yiwuwar fuskantar mummunan yanayin jin kai, idan har makamashin da ake amfani da shi a zirin Gaza ya yanke nan da kwanaki 10 masu zuwa.

Mr. Haq ya ce, akwai bukatar masu ba da tallafi su hanzarta gabatar da taimako, ganin cewa a yanzu haka kusan falasdinawa miliyan 2 ne ke zaune a zirin na Gaza, kuma sama da rabin su yara ne kanana, dake samun wutar lantarki da ba ta wuce sa'o'i 8 a rana.

Ya ce, a bana, ana bukatar dalar Amurka miliyan 6.5 domin sayen litar mai miliyan 7.7 wadda ake matukar bukata a yankin. Wannan adadi shi ne kuma mafi kankanta da ake bukata, idan har ana fatan kaucewa rushewar ayyukan hidima da ake samarwa ga al'ummun yankin.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China