in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin MDD a Gabas ta Tsakiya ya yi gargadi game da barkewar rikici a Gaza
2018-04-27 09:44:04 cri

Babban jami'in tsare tsare na ayyukan wanzar da zaman lafiyar MDD a Gabas ta Tsakiya Nickolay Mladenov, ya nuna damuwa game da yiwuwar barkewar tashin hankali a zirin Gaza, bayan da aka kwashe makwanni ana zaman dar dar a kan iyakar Isra'ila.

Mladenov ya shaidawa kwamitin tsaron MDD a jiya Alhamis cewa, matsalolin tsaro da na ci gaba, da tabarbarewar ayyukan jin kai, tare da rashin tabbas a fannin siyasa sun sanya zirin na Gaza zama wani wuri mai hadari. Ya ce, duk da halin da ake ciki a wannan yanki, akwai bukatar daukar dukkanin matakan da suka wajaba, na kare barkewar tashin hankali.

Jami'in ya kara da cewa, cikin makwanni 4 da suka gabata, dubban Falasdinawa na ci gaba da taruwa a Gaza kusa da kan iyakar Isra'ila, a wani mataki na matsin lamba, game da zargin mamayar yankunan su da Isra'ilar ke yi.

Ana dai hasashen masu zanga zangar za su ci gaba da jerin gwano har zuwa ranar bikin samun 'yancin kan Yahudawan Isra'ila, wato ranar 14 ga watan Mayu, kuma mai yiwuwa ne zanga zangar ta yadu zuwa yamma da kogin Jordan, da ma wasu sauran yankuna.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China