Gwamnatin hadin kan Falasdinu ta fara sauya fasalin ma'aikatu da sassa a zirin Gaza, a wani bangare na yarjejeniyar da aka cimma makon da ya gabata a Masar.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar a hukumance, bayan firaministan Falasdinu Rami Hamdallah, ya jagoranci taron majalisar zartarwa na mako-mako a yankin yammacin kogin Jordan.
Sanarwar ta ce, tuni kwamitocin zartarwa na hukumomin gwamnatin da na tsaro da iyakoki suka fara aiki a Gaza.
Ta kara da cewa, gwamnati na da wani cikakken tsari da za ta mika ga dukkan ma'aikatunta dake zirin Gaza, inda ta kara da cewa, daga mako mai zuwa, za a fara gudanar da taron majalisar zartarwar a Gaza da kuma yankin yammacin da kogin Jordan.
A ranar Litinin ne kwamitin gwamnatin Falasdinu ya fara shirye-shiryen mika iyakoki a zirin Gaza, kamar yadda yarjejeniyar ta birnin Alkahira ta tanada. (Fa'iza Mustapha)