in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya ta musanta bidiyon da ake ikirarin na gidan tsohon shugaban hukumar DSS ne
2018-08-14 09:49:53 cri

Gwamnatin Nijeriya ta musanta ikirarin da ake cewa, jami'an hukumar tsaro ta farin kaya DSS, sun gano kudi da muggan makamai a gidan Lawal Daura, tsohon shugaban hukumar DSS da aka sallama daga aiki.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, kakakin hukumar Tony Opuiyo, ya ce bidiyon da ake ikirarin na gidan tsohon shugaban hukumar ne na bogi ne.

Abubuwan da ake zargin an gano a gidan sun hada da kananan makamai daban daban guda 400 da bindigogi da dubban katunan zabe na mutanen Jamhuriyar Niger da suka kaura zuwa Nijeriya.

Tony Opuiyo, ya ce zuwa yanzu, jami'an hukumar ko na wata hukumar tsaro, ba su gudanar da irin wannan aiki a gida ko ofishin tsohon shugaban hukumar ba.

A wani bidiyon na daban da ake yadawa, an ga wasu mutane da aka yi ammana jami'an hukumar DSS ne suna kokarin sa karfi wajen bude wani asusu dake shake da kudi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China