in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ITTF za ta taimakawa Najeriya wajen daga matsayin wasan kwallon tebur
2018-08-09 09:30:32 cri

Hukumar kula da wasannin kwallon tebur ta duniya ITTF ta sanar a jiya Laraba cewa, za ta daga martabar wasannin kwallon tebur na shekara shekara wanda za'a bude a Najeriya a shekarar 2019.

Daga matsayin wasan yana nufin za'a kara samar da karin kyautukan kudade, da daga matsayin wasan zuwa matsayin wanda ke sahun gaba a duniya, da samar da yanayi mai inganci ga 'yan wasa da kuma samar da shirye shiryen talabijin.

Za'a bude wasan na Najeriya ne daga ranar 8-12 ga watan Agusta a Lagos, cibiyar kasuwancin kasar.

Kimanin biranen duniya 9 ne suka shiga gasar ta wannan karon da suka hada da Najeriya, Korea ta arewa, Oman, Portugal, Paraguay da Canada.

Jerin wasannin kimanin 17 na shekarar 2019, sun hada da birane 9 wadanda ba su taba daukar bakuncin wasannin ba kuma za'a rarraba su zuwa bangarori biyu biyu a karon farko, inda babban bangare ake kiransa da suna Challenge Plus.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China