in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Nijeriya ta yi tir da kawanyar da jami'an tsaro suka yi wa ginin majalisar dokokin kasar
2018-08-08 09:55:37 cri

Fadar shugaban Nijeriya, ta bayyana kutsen da jami'an tsaro na farin kaya suka yi wa majalisar dokokin kasar ba tare da amincewarta ba a matsayin take doka.

Mukaddashin shugaban kasar Yemi Osinbajo, ya ce an yi wa majalisar dokokin kawanya ne ba tare da sanin fadar shugaban kasa ba, yana mai bayyana matakin a matsayin wanda bai dace ba, da kuma ba za a taba amincewa da shi ba.

Osinbajo ya kuma tabbatarwa 'yan Nijeriya cewa, za a hukunta duk wanda ke da hannu cikin aikin.

A cewarsa, za a lalubo dukkan jami'an tsaron da ke da hannu cikin lamarin domin su fuskanci hukuncin da ya dace.

Da safiyar jiya Talata ne 'yan sanda da jami'an hukumar tsaro ta farin kaya, suka rufe babbar kofar shiga harabar majalisar dokokin kasar, al'amarin da ya hana mambobin majalisar da ma'aikata shiga ciki.

Daga bisani, jami'an tsaron sun bar mambobin majalisar sun shiga, yayin da suka hana 'yan jarida da sauran ma'aikata. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China