in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Morocco ta yi nasarar gwajin jirgin kasa mafi sauri a Afrika
2017-12-29 09:43:25 cri

Hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Morocco ta sanar a jiya cewa, kasarsa ta yi nasarar gudanar da gwajin jirgin kasa mafi sauri a nahiyar Afrika.

Hukumar ta ce, gwajin na baya-bayan nan da aka yi a farkon makon nan ya cimma nasara, inda jirgin ya yi tafiyar kilomita 320 cikin sa'a 1, tana mai bayyana shi a matsayin abun da ya shiga tarihin kasar.

Ko a watan Oktoban da ya gabata, Morocco ta yi gwajin jirgin a gaban ministan harkokin wajen Faransa Jean Yves Le Drian, wanda kasarsa ta ba da wani kaso na aikin, inda jirgi ya yi tafiyar kilomita 275 cikin sa'a 1.

Tun farkon shekarar nan ne, aka fara gwajin layin dogon mai hannun biyu da kasar Faransa ta shimfida wanda ya hada biranen Tangier da Casablanca, inda za a kaddamar da shi a lokacin rani. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China