in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yayin da aka kiara tsaurara sa ido, kasar Sin ta samu raguwar masu sayen hannayen jari domin samunkazamar riba
2018-08-11 16:18:31 cri
Kasar Sin ta samu gagarumar raguwar ayyukan sayen hannayen jari ta bayan fage domin samun kazamar riba, yayin da hukumomin sa ido kan takardun hannun jari ke kara zage damtse wajen yaki da take dokokin kasuwanci.

kiddigar da hukumar kula da hannayen jari ta kasar Sin ta fitar, ta ce ayyukan masu sayen hannayen jari ta bayan fage domin samun kazamar riba ya sauka da kaso 50 bisa 100 cikin rabin shekarar nan, idan aka kwatanta da bara. An samu raguwar aikata laifin ne saboda nasarorin yaki da shi da aka yi ta samu a bara.

Wani jami'in hukumar ya ce an yi nasarar magance matsalar a sassan kula da kadarori na kamfanonin inshora da kamfanonin hada-hadar hannayen jari.

Sayen hannayen jari ta bayan fage na nufin masu kula da hanayen jari su saye hannayen jari ta asusunsu na kansu, kafin cibiyoyin hada-hadar kudin da suke wa aiki, domin su sayar su samu kazamar riba bayan farashi ya tashi. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China