Leila Gharagozloo-Pakkala, wadda ta yi wannan kira, yayin wani taron lalubo hanyoyin warware matsalar karancin abinci mai gina jiki tsakankanin kananan yara dake gudana a birnin Nairobin kasar Kenya, ta ce, duk da irin ci gaban da aka samu a shekarun baya bayan nan, akwai yara 'yan kasa da shekaru 5 da yawan su ya kai miliyan 55, wadanda ke fama da karancin abinci mai gina jiki a wannan shiyya.
Jami'ar ta kara da cewa, da dama daga rukunin wadannan yara na shafe kwanaki 1,000 na farkon rayuwar su ba tare da samun abincin mai nagarta ba. Mahalarta taron na wannan karo dai za su shafe kwanaki 4, suna nazartar hanyoyin dakile wannan matsala, sun kuma kunshi wakilai da masana daga kasashen Afirka a kalla 35.
Kafin kammalar taron, ana sa ran mahalartan sa za su duba yiwuwar kara zuba jari a fannin samar da abinci mai gina jiki ga yara ta hanyar hadin gwiwa da hukumomin cikin gida, da na sassa masu zaman kan su.(Saminu)