in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira ga Japan da ta tuna ta'asar da ta aikata a lokacin yakin duniya na biyu
2018-08-10 10:06:04 cri

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi kira ga shugabannin kasashen duniya da su yiwa Allah su hanzarta kwance damarar makaman nukiliyar da suka mallaka, a wani mataki na samar da zaman lafiya a duniya.

Guterres na wannan kiran jiya Alhamis yayin da yake jawabi a bikin cika shekaru 73 da Amurka ta jefa makamin kare dangi a birnin Nagasaki na kasar Japan.

Jami'in na MDD ya ce, yadda shirin kwance damarar ke tafiyar hawainiya ko ma ya cije, shi ya tilastawa MDD kaddamar da yarjejeniyar haramta makaman kare dangin a shekarar da ta gabata, lamarin da ya bata ran wasu kasashe.

Shi ma magajin birnin Nagasaki ya bukaci gwamnatin Japan da ta goyi bayan yarjejeniyar haramta makaman nukiliya ta duniya, wadda ta fara aiki a shekarar da ta gabata.

Da misalin karfe 11.02 na rana, agogon Japan ne wato dai-dai lokacin da jirgin yakin Amurka ya jefa makaman kare dangin da ya halaka mutane kusan 74,000 a Nagasaki ya zuwa karshen shekarar 1945, mahalarta bikin suka yi shiru na minti guda don tunawa da harin da ya faru.

Bayan harin da aka kai a birnin Nagasaki, Amurkar ta sake jefa wani makamin nukiliya a ranar 6 ga watan Agusta kan birnin Hiroshima, duk domin kawo karshen yakin duniya na biyun, tare da tilastawa Japan ta mika wuya ba tare da an mamaye ta ba, har ma a kai ga asarar rayukan mutane da dama.

Babban sakataren MDD Antonio Guterres shi ne, magatakardan MDDr dake kan mulki da ya taba halartar bikin da ake shiryawa a ko wace shekara.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China