Shinzo Abe ya ce, bangarorin biyu sun kuma sake tabbatar da hadin gwiwa tsakaninsu domin kalubalantar Koriya ta arewa da ta yi watsi da shirinta na kera makaman nukiliya da makamai masu linzami. Ban da wannan kuma, Abe ya ce, a yayin wayar tasu, Abe ya bukaci Trump sau da dama da ya tabo batun yin garkuwa da 'yan Japan da Koriya ta arewa ta kan yi a karnin da ya gabata.
Rahotanni na cewa, a ran 24 ga wannan wata ne, shugaba Trump ya rubuta wata wasika ga Kim Jong-un inda ya sanar da soke ganawar tasu da aka shirya yi a ran 12 ga watan Yuni a kasar Singapore. Amma a ran 26 ga wata, Trump ya ce za a gudanar da ganawar kamar yadda aka shirya a baya. (Amina Xu)