in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guterres na bibiyar batun tilastawa shugaban 'yan adawar Zimbabwe komawa gida
2018-08-10 09:42:50 cri

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, yana sa ido sosai game da yanayin da ake ciki a Zimbabwe a jiya Alhamis, biyo bayan zargin da ake na tilastawa shugaban 'yan adawar kasar komawa gida, bayan ya nemi mafaka a Zambiya dake makwabtaka da kasar.

Kakakinsa Farhan Haq, ya ruwaito cewa, Antonio Guterres ya ce za su rika bibiyar abun da zai faruwa bayan komawar madugun 'yan adawar wato Tendai Biti, da aka hanawa samun mafaka a kasar Zambiya.

Tendai Biti ya tsere ne a lokacin da 'yan sanda ke nemansa tare da wasu shugabannin 'yan adawar, bisa zarginsu da kisa rikicin a makon da ya gabata, wanda ya samo asali daga nasarar lashe zaben kasar da jam'iyyar Zanu PF mai mulki ta yi.

Mutane 6 ne suka mutu yayin zanga-zangar da ta biyo bayan zaben da aka yi a karon farko bayan sojoji sun tumbuke shugaba Robert Mugabe mai shekaru 94 da ya dade a kan karagar mulki. Shugaban Jam'iyyar Zanu PF Emmerson Mnangagwa ne ya lashe zaben, inda ya doke abokin takararsa kuma shugaban jam'iyyar adawa ta MDC wato Nelson Chamisa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China