Sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya nuna damuwa sakamakon harin da aka kaddamar kan taron gangamin jam'iyya mai mulkin kasar Zimbabwe wanda shugaban kasar Emmerson Mnangagwa da sauran jiga-jigan jamiyyar suka halarta.
Hukumomin kasar Zimbabwen sun bayyana harin da aka kaddamar na ranar Asabar a birnin Bulawayo da cewa yunkuri ne na hallaka shugaba Mnangagwa.
Kakakin MDD Stephane Dujarric, ya ce Guterres ya yi Allah wadai da harin, kana ya bukaci a binciko wadanda ke da hannu da kuma gurfanar da su a gaban shari'a, tare da fatan samun sauki cikin hanzari ga wadanda suka jikkata a harin.(Ahmad Fagam)