in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan Zimbabwe za ta samu ci gaba cikin zaman lafiya
2018-08-02 19:34:56 cri

Yau Alhamis a nan birnin Beijjing kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana cewa, kwanakin baya aka gudanar da babban zaben shugaban kasa da 'yan majalisar dokoki da kuma kansilolin kananan hukumomin kasar ta Zimbabwe, lamarin da zai yi babban tasiri ga harkokin siyasar kasar.

Amatsayinta na aminiyar Zimbabwe, har kullum kasar Sin tana mai da hankali matuka kan yanayin da take ciki, a don haka gwamnatin kasar Sin ta tura wata tawagar wakilai zuwa kasar bisa gayyatar gwamnatin Zimbabwe, inda wakilan kasar Sin suka ga yadda al'ummar kasar Zimbabwe suka nuna kwazo da himma kan zabukan, haka kuma suka gudanar da zabukan cikin kwanciyar hankali da tsari, kasar Sin tana fatan masu ruwa da tsaki na bangarori daban daban na kasar za su yi hada kai domin cimma burin raya kasarsu cikin lumana.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China