in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
SADC ta yaba da yadda aka gudanar da zabe a Zimbabwe
2018-08-01 19:25:46 cri

Tawagar SADC dake sa-ido a zabukan kasar Zimbabwe da aka kammala, ta yaba da yadda zabukan suka gudana cikin lumana da tsari. Sannan ta yi kira ga hukumar zaben kasar ZEC da ta martaba dokokin zabe kamar yadda ya ke kunshe cikin sabon kundin tsarin mulkin kasar, kana ta bullo da matakan da za su tabbatar da cewa 'yan kasar dake zaune a ketare sun yi zabe a nan gaba.

A wata kwarya kwaryar sanarwa da tawagar ta fitar, ta ce an gudanar da zabukan kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada kuma cikin yanayi na zaman lafiya da ya baiwa 'yan kasar ta Zimbabwe damar sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya ba su na yin zabe.

A ranar Litinin ne dai al'ummar kasar Zimbabwe suka kada kuri'a don zaben shugaban kasa, da 'yan majalisun dokoki da kuma kansiloli. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China