in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Ghana ya yi garanbawul a majalisar ministan kasar
2018-08-10 09:36:19 cri

Shugaba Nana Akufo-Addo ya yi garambawul a majalisar ministocin kasar, inda ya nada wasu sabbin ministoci, ciki har da sabon ministan makamashi.

Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar a jiya Alhamis, ta bayyana cewa, yanzu ministan filaye da albarkatun kasa John Peter Amewu shi ne ministan makamashi, yayin da Kwaku Asomah-Cheremeh ya zama ministan filaye da albarkatun kasa.

Haka kuma Amewu ya maye gurbin Boakye Agyarko wanda shugaban kasar ya kora a ranar Litinin, sakamakon takaddamar da ta kunno kai a game da sake bibiyar yarjejeniyar samar da makamashi da aka cimma tsakanin gwamnatin Ghana da kamfanin AMIERI Resources.

Shi kuma Mustapha Abdul-Hamid wanda mataimakinsa Kojo Oppong-Nkrumah ya maye gurbinsa a matsayin ministan watsa labarai, yanzu shi ne ministan babban birni da raya Zongo, yayin da tsohon minista Boniface Abubakar Saddique ya koma ofishin mataimakin shugaban kasa a matsayin karamin minista.

Baki daya dai, shugaban ya yi canje-canje guda 15 ne, baya ga jami'an larduna da mataimakan ministoci da aka nada.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China