in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Ghana da FIFA sun sha alwashin warware matsalar jagorancin kwallon kafa a Ghana
2018-07-05 09:53:27 cri

Ministan wasanni da harkokin matasa na kasar Ghana Isaac Kwame Asiamah, ya ce gwamnatin kasar, da kuma hukumar FIFA, sun amince da daukar wasu matakai, na inganta jagorancin kwallon kafa a Ghana. Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai.

Isaac Kwame Asiamah, ya ce matakan da za a dauka, sakamako ne na wani taron wakilan gwamnatin, da kuma na hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, wanda ya gudana a birnin Zurich na kasar Switzerland a Juma'ar da ta gabata.

Hakan ya biyo bayan dakatarwar wucin gadi daga harkokin wasannin kwallon kafa da FIFAr ta yiwa kasar, bayan da wani kwarya kwaryar bincike ya nuna yadda wasu jami'an wasan kasar ke da hannu dumu dumu, a badakalar cin hanci da rasha wajen gudanar da wasan na kwallon kafa a kasar.

Kafin kammala dukkanin bincike, sassan biyu sun amince da mika ragamar harkokin wasannin kasar hannun wani hamshakin dan kasuwa mai sha'awar wasanni mai suna Kofi Amoah, da kuma daraktan tsare tsare a hukumar kwallon kafar kasar Francis Oti Akenten, a matsayin wata hanyar ci gaba da tuntuba, tsakanin hukumar kwallon kafar kasar GFA, da hukumar FIFA, da ta wasannin kwallon Afirka ta CAF.

Sanarwar ta ce, ana sa ran hakan zai kai ga warware matsalolin dake addabar harkokin wasannin kasar. Kafin hakan, gwamnatin kasar ta yi kira ga daukacin masoya kwallon kafa a Ghana da su kai zuciya nesa, su kuma ba da hadin kai yayin da ake daukar kwararan matakan maido da harkokin wasannin kwallon kafar kasar ta Ghana kan kyakkyawar turba.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China