in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana na shirin daukar matakan kawo karshen kayayyakin dake kunshe da sinadarin mercury
2018-08-09 10:27:58 cri

Kasar Ghana na shirin daukar matakan kawo karshen samar da kayayyakin dake kunshe da sinadarin mercury bisa yarjejeniyar kasa da kasa game da kare lafiyar bil-Adama da muhalli daga gubar da ke fita da sinadarin mercury, kamar yadda jami'in kasar ya sanar a ranar Talata.

Sam Adu-Kumi, daraktan cibiyar dake kula da sinadarai da kare muhallai ta kasar (EPA), ya jaddada bukatar gaggauta ilmantar da jama'ar kasar da wayar da kansu game da irin matsayar da mahukuntan kasar suka cimma kan wannan batu.

A cewarsa, wannan batu yana da muhimmanci bisa la'akari da illar da sinadarin mercury ke iya haifarwa ga muhalli da rayuwar bil adama.

Ya fadawa manema labarai a lokacin taron karawa juna sani cewa, sinadarin Mercury da ya watsu a sararin samaniya, zai lahanta muhalli da abinci da tsirra da dabbobi, kana daga karshe ma zai lahanta rayuwar dan adam da zarar suka shake shi.

An amince da yarjejeniyar kasa da kasa da ta shafi kare lafiyar bil adama da muhalli daga fuskantar illolin sinadarin mercury ne a taron wakilan kasa da kasa da aka gudanar a Kumamoto na Japan a shekarar 2013.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China