in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Zhanshu yana fatan za a ciyar da hulda tsakanin Sin da Afirka ta Kudu gaba
2018-06-20 20:30:38 cri

A yau Laraba ne a nan birnin Beijing, shugaban kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Li Zhanshu ya yi ganawa da shugaban majalisar dokokin kasar Afirka ta Kudu Cedric Frolick, inda ya bayyana masa cewa, yana sa ran kasashen biyu za su yi hadin gwiwa, domin gudanar da taron kolin kasashe mambobin kungiyar BRICS a Johannesburg, da taron kolin dandalin hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka a Beijing lami lafiya, kana za su yi kokari tare, domin aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya yadda ya kamata. Ban da haka kuma, sassan biyu za su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakanin hukumomin tsara dokokin kasashen biyu, ta yadda za su ciyar da huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare dake tsakaninsu gaba kamar yadda ake fata.

A nasa bangaren, Frolick ya ce, kasarsa tana fatan za ta kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin, bisa tsarin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da na kungiyar BRICS, wanda ta haka ne za a kai ga raya huldar su daga duk fannoni.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China