in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Afirka ta kudu ta karyata wasu rahotanni game da murabus din kakakinta
2018-07-25 09:39:56 cri

Majalisar dokokin kasar Afirka ta kudu ta karyata wasu rahotanni dake wadari cewa, kakakinta Baleka Mbete ta yi murabus daga mukaminta.

Mai magana da yawun majalisar Moloto Mothapo ya ce, wannan magana karya ce tsagwaronta. A ranar Litinin ne dai kafar watsa labaran Afirka ta kudu ta ba da rahoton cewa, kakakin majalisar Mbete ta sanar da yin murabus a karshen mako, cewa ba za ta koma majalisar ba, bayan zabukan kasar na shekarar da ta gabata. Wannan rahoto ya janyo mabanbantan ra'ayoyi.

Sai dai kuma majalisar ta mayar da martani, tana mai cewa za a dade ana tunawa da Mbete a matsayinta na jagorar majalisar wadda ba ta nuna wariya ga kowane bangare.

A hannu guda kuma jam'iyyun adawa sun zargi Mbete da yunkurin shafawa tsohon shugaban kasar Jacob Zuma kashin kaji ta hanyar bincikarsa a majalisar game da badakalar kudade.

Amma mai magana da yawun majalisar dokokin kasar, ya ce Mbete ta sanar a yayin babban taron jam'iyyar ANC mai mulkin kasar cewa, za ta ci gaba da bautawa jama'a, da mazabarta ta Khayelitsha dake Cape Town har zuwa bayan zabukan shekarar 2019. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China