in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan bindiga sun yi garkuwa da kauyawa 15 a arewa maso yammacin Najeriya
2018-07-30 19:14:32 cri

Rahotanni daga Najeriya na cewa, wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da a kalla kauyawa 15, lokacin da suka kai hari cikin karshen mako a yankin Maradun dake jihar Zamfara a arewa maso yammacin kasar.

Kakakin majalisar dokokin jihar Sanusi Rikiji ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho cewa, har yanzu ba a san inda mutanen da aka yi garkuwa da su suke ba.

Ya ce, a baya-bayan nan 'yan bindigar sun kwace a kalla kauyuka da garuruwa a kalla 18 a sama da gundumomin uku dake jihar. A don haka akwai bukatar a sake duba yanayin tsaron da jihar ke ciki.

A jiya Lahadi ne gwamnatin Najeriya ta sanar da tura sama da sojoji 1,000 don magance matsalar hare-haren da jihar ta Zamfara ke fuskanta.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China