in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Nijeriya ta nada sabon mukaddashin shugaban hukumar DSS
2018-08-08 09:40:19 cri

Gwamnatin Nijeriya ta tabbatar da nadin Matthew Seiyefa, jami'i mafi matsayi a hukumar tsaro ta farin kaya DSS, a matsayin mukaddashin shugaban hukumar.

Matthew Seiyefa, ya gana da mukaddashin shugaban kasar Yemi Osinbajo a fadar gwamnatin kasar, bayan an sallami tsohon shugaban hukumar Lawal Daura.

Yemi Osinbajo, ya ba da umarnin sallamar Lawal Daura ne bisa yi wa tsaron kasa karan tsaye, sanadiyyar kawanyar da jami'in hukumar ta farin kaya da suka rufe fuskokinsu suka yi wa ginin majalisar dokokin kasar.

Matthew Seiyefa, wanda ya fito daga jihar Bayelsa mai arzikin man fetur, ya taba rike mukamin daraktan cibiyar nazarin harkokin tsaro ta kasar, kafin daga bisani a mayar da shi hedkwatar hukumar tsaro ta farin kaya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China