in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dan takarar jam'iyya mai mulki a Najeriya ya lashe zaben gwamnan jihar Ekiti
2018-07-16 09:21:37 cri

Hukumar zaben Najeriya ta sanar cewa, mutumin da ya tsaya takarar gwamnan jihar Ekiti dake kudu maso yammacin Najeriyar a jam'iyya mai mulkin kasar ne ya lashe zaben gwamnan wanda ya gudana a ranar Asabar din da ta gabata.

Idowu Olayinka, babban jami'in tattara sakamakon zaben kuma mataimakin shugaban jami'ar Ibadan, ya ce Kayode Fayemi, tsohon ministan ma'adanai kana 'dan takarar jam'iyyar (APC) mai mulki ya samu kuri'u 197,459, inda hakan ya ba shi nasarar lashe zaben.

Olayinka ya sanar da sakamakon zaben ne a helkwatar hukumar zaben dake birnin Ado-Ekiti a jiya Lahadi.

Dan takarar babbar jam'iyyar adawa ta (PDP), Kolapo Olusola, shi ne ya zo na biyu da yawan kuri'u 178,121.

Sai dai jam'iyyar ta PDP, ta yi watsi da sakamakon zaben, inda ta yi zargin cewa, an tafka kura kurai a zaben kuma ta yi zargin an kai hari kan wasu daga cikin 'yayanta da magoya bayanta.

Fayemi zai karbi ragamar shugabancin jihar daga hannun gwamnan jihar mai ci, Ayo Fayose, a ranar 16 ga watan Oktoban shekarar 2018.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China