in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na tuntubar abokan huldarta dangane da sabbin hanyoyin kara hadin gwiwa tsakaninta da Afrika
2018-03-20 09:46:51 cri

Mai kula da harkokin shirin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen nahiyar Afrika FOCAC, wato Zhou Yuxiao, ya ce kasar Sin na tuntubar abokan huldarta a nahiyar Afrika game da yiyuwar yaukakka huldar dake tsakaninsu karkashin shirin na FOCAC.

Zhou Yuxiao, ya ce biyo bayan aiwatar da tsare-tsare 10 da taro tsakanin shugabannin nahiyar Afrika da na kasar Sin da ya gudana a shekarar 2015 ya gabatar, kasar Sin na tuntubar shugabannin Afrika kan kara sabbin fannonin hadin gwiwa don karawa dangantakarsu armashi.

Yayin wani taron manema labarai a Nairobin Kenya, Zhou Yuxiao ya ce an samu nasarori masu gamsarwa dangane da aiwatar da tsare-tsaren, inda ya ce, sun yi aiki tukuru wajen aiwatar da tsare-tsaren a dukkan fannoni.

Jami'in na kasar Sin na ziyara a kasashen gabashin Afrika ne don ganawa da shugabanni da jami'an kasashen da kuma 'yan kasuwa Sinawa dake zaune a can, har ma da masana, kan yadda za a inganta dangatakar kasar Sin da kasashen Afrika.

Ya ce, shirin ya ta'allaka ne a kan gudanar da ayyuka, kuma yana shirin inganta hadin gwiwar bangarorin biyu bisa sabbin fannoni kamar na shawarar "Ziri daya da hanya daya"

Bugu da kari, ya ce za a bukaci kasashen Afrika su mika jerin ayyukan da za su cancanci samun kudi karkashin shirin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China