in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin Foton na kasar Sin ya fara hada manyan motocin dakon kayayyaki a Kenya
2018-01-25 10:56:13 cri

Kamfanin hada motoci na kasar Sin Foton, a jiya Laraba ya kammala aikin hada manyan motocin dakon kayayyaki a kasar Kenya, a wani mataki na kara samarwa kananan kasuwannin cikin gida a kasar ta Kenya damammaki.

Sun Qingzhong, babban manajan kamfanin Foton na kasar Sin dake Kenya, ya bayyana a birnin Mombasa cewa, kamfanin yana ta kokarin neman fitar da kayayyakinsa don yin gogayya a kasuwannin duniya, ya riga ya tsara wani ingantaccen tsarin aiki a Kenya da ma Afrika.

Sun ya ce, kamfanin zai dinga harhada motocinsa a cibiyar hada motoci ta (AVA) dake Miritini, a yammacin birnin Mombasa.

Ya ce, kamfanin Foton a shirye yake ya dinga gudanar da harkokinsa a kananan yankuna, inda zai dinga samarwa abokan huldarsa kayayyaki masu matukar inganci.

Kamfanin zai kuma dinga samar da kayan gyara na motocin, da ayyukan hidimar kula da motocin da aka saya, kana zai kara samar da kudaden haraji ga kasar, da kuma samar da guraben ayyuka masu yawa, sannan zai kara habaka ci gaban tattalin arzikin kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China